Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa an sami wani babban kabari dake dauke da mutane 49 a Arewa maso gabashin kasar Kwango.
Mataimakin kakakin majalisar Farhan Haq ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin New na kasar Amurka, inda yace an sami kaburran ne a wasu kauyuka 2 a yankin Ituri dake da nisan kilo miter 30 da birnin Bunia.
An sami adadin mutane 42 da suka hadar da yara 6 a wani babban kabari a kauyen Nyamamba, haka kuma an ga wasu gawarwaki maza 7 a kauyen Mbogi, a cewar Haq.
Hukumomin yankin sun bayyana cewa kungiyar ‘yan bindiga ta CODECO sun kuma yi awon gaba da wasu mata a hare-haren da aka kai kauyukan.
Ko dai a watan Yulin daya gabata, kungiyar ta CODECO su 7 suka sanar da kawo karshen cin zarafin fararen hula a garin Ituri, musamman Djugu inda suke da karfi. Amma duk da haka suka cigaba da kai hare-hare a yankin.
Akalla mutane 195 ne aka hallaka tun watan disamba a jirin hare-haren da ake zargin kungiyar CODECO da wasu kungiyoyi mas dauke da makamai a cewar MDD. Haka kuma fiye da mutane miliyan 1.5 suka rasa matsugunnin su a lardin Ituri biyo bayan hare-haren.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 23 hours 20 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 1 hour 2 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com