Babban bankin Najeriya CBN ya ce zai dauki tsattsauran mataki kan wasu bankuna a Jihar Kano, saboda kin zuwa su karbi sabbin takardun naira da ya samar.
CBN reshen Jihar ta Kano ya jaddada matsayarsa kan cewa karshen watan nan na Janairu zai daina karbar tsaffin kudaden kamar yadda ya sanar tun bara.
Al’umma a fadin Najeriya na ta kokawa kan karancin sabbin kudaden da bankin ya kaddamar a bankuna, baya ga korafin da suke yi na rashin bayar da cikakken wa’adi domin mayar da tsofaffin kudaden bankuna.
Shugaban CBN reshen Jihar Kano Malam Umar Ibrahim Biyu a tattaunawarsa da manema labarai ya ce, akwai isassun sabbin takardun kudaden bankuna kawai ake jira su je su karba.
A cewarsa wasu kuwa na hadawa sabbi da tsofaffi, amma binciken da suka fara gabatarwa ya sanya an samu gagarumin sauyi.
A yanzu idan kaje ATM za ka samu sababbin kudade a kusan ko ina a fadin Jihar Kano.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 20 hours 44 minutes 58 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 22 hours 26 minutes 23 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com