Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta musanta karin kudin Man fetur

Gwamnatin Najeriya ta musanta yin ƙarin farashin man fetur, duk kuwa da ƙaruwar farashin man a faɗin ƙasar.

Kafafen yaɗa labarai  sun ambato ƙaramin ministan albarkatun man fetur na ƙasar Timipre Sylva a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ta hannun mai taimaka masa kan kafofin yaɗa labarai, cewa Shugaban ƙasar bai amince da wani ƙarin sabon farashi ga man fetur ɗin ba.

A ranar Juma’ar ne dai shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen Jihar Kano Bashir Danmallam ya tabbatar wa manema labarai ƙarin farashin man fetur ɗin da kashi 8.8 cikin 100, inda ya ce sun samu umarni daga gwamnatin tarayya.

To sai dai sanarwar da ƙaramain ministan man fetur ɗin ya fitar ta ce ”babu wani dalili da shugaban ƙasar zai amince da ƙarin farashin man a daidai wannan lokaci”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”gwamnati ba za ta amince da ƙarin farashin man fetur a asirce ba, ba tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki a fannin man fetur din ba”.

”Dan haka shugaban ƙasa bai umarci ƙungiyar dillalan man fetur da cewa su ƙara kuɗin man fetur ɗin ba”, in ji sanarwar

Haka kuma sanarwar ta ambato ministan na yin kira ga ‘yan ƙasar da su kwantar da hankulansu, su kuma zama masu bin doka, a yayin da gwamnatin ƙasar ke iya bakin ƙoƙarinta wajen wajen dawo da al’amuran rarraba man kamar yadda aka saba a baya.

Tun cikin watan Oktoban bara ne dai ake fuskantar ƙarancin man fetur a wasu sassan ƙasar, lamarin da ya haddasa sayar da man a mabambantan farashi a sassan ƙasar wadda ta fi kowacce ƙasa arzikin man fetur a nahiyar Afirka.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 32 minutes 53 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 14 minutes 18 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com