Gwamnatin jihar Kano tabbatar da barkewar annobar diphtheria a kananan hukumomi 13 dake fadin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr Aminu Tsanyawa ne ya bayyaba hakan yayin da yake bayani kan barkewar cututtukan na Diphtheria da cutar Lassa a ranar Asabar.
Yace an sami mutane 100 da ake zargin sun kami da cutar yayin 3 suka mutu.
“Daga ranar 20 ga watan Janairun 2023 mun sami adadin mutane 100 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi 13 dake jihar kano.
Read Also:
Wanda suka hadar da ”Ungogo, Nassarawa, Bichi, Dala, Dawakin Tofa, Dawakin Kudu, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kiru, Rano, and Gwarzo.
“Cikin mutane darinda ake zargi sun kamu da cutar gwaji ya tabbatar da mutane 8 inda ake dakon sauran sakamakon.
“mun rasa rayukan mutane 3 cikin wadanda aka tabbatar da sun kamu da cutar.
Tsanyawa ya kara da cewa yanzu haka majinyata 27 na karkashin kulawar likitoci inda aka sallami 41 bayan sun warke.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 56 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 37 minutes 55 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com