Babban bankin Najeriya CBN ya ce babu gudu babu ja da baya game da wa’adin da ya sanya na daina amfanin da tsoffin takardun kuɗin ƙasar daga ranar 31 ga watan Janairu.
Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka bayan ganawar kwamitin babban bankin kan tsare-tsaren kuɗi.
Mista Emefiele ya jaddada cewa babban bankin ya bayar da wadataccen lokaci ga ƴan ƙasar da su mayar da tsoffin kuɗadensu zuwa bankunan ƙasar domin musanya su da sabbi.
Gwamnan babban bankin ya ƙara da cewa tun bayan sauya fasalin takardun kuɗin uku an samu raguwar garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
Yana mai cewa kawo yanzu babban bankin ya karɓi tsoffin takardun kuɗi da adadinsu ya kusa naira tiriliyan 1 da biliyan dari 5, tare da fatan cewa za su iya kai wa tiriliyan biyu kafin cikar wa’adin da bankin ya saka.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 22 hours 33 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 14 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com