Home General ‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da Dagaci a Jihar Kaduna

‘Yan Bindiga sun yi garkuwa da Dagaci a Jihar Kaduna

Rahotannin daga jihar kaduna na bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Chief Joshua Ahmadu dagacin
Garin Chawai dake karamar Hukumar Kauru a jihar kaduna.
Shugaban kungiyar cigaban Chawai Mista Abel Adamu ne ya tabbatar da sace dagacin a ranar Laraba.
Adamu ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin CDA yace an dauke Dagacin ne a daren talata bayan da ‘Yan bindigar suka kutsa cikin gidan sa dake Zambina.”
” ‘Yan bindigar sun shiga gidan dagacin ne da misalin karfe 9:30pm inda sukayi awon gaba da shi. A cewar Adamu.
Daga bisani Shugaban kungiyar ya bayyana takaicin sa bisa wannan aiki sannan kuma ya bayyana yadda suke fafutuka wajen ganin sun kubutar da shi ba tare da wani abu ya same shi ba.

“tuni mun sanar da masu ruwa da tsaki da jami’an tsaro wanda tuni sun fara gudanar da abin da ya dace domin kubutar da shi.
“muna kira da daukacin Al’ummar garin Tsam maza da mata dasu yi addu’ar dawowar shugaban mu cikin koshin lafiya.

Sanarwar ta kuma kalubalanci matasa dake karkashin Masarautar dasu zage dantse wajen ganin sun tabbatar da tsaro kada wannan lamari ya sake faruwa.
“ya kamata mu tsaya da kafar mu domin tabbatar da tsaro da kubuta daga matsalar rashin sa.

NAN

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp