Shugaban Majalisar Wakilan, Femi Gbajabiamila ya bayyana fushinsa kan yadda gwamnan babban bankin ya ki halartar zama tare da wani kwamitin wucen-gadi na majalisar karkashin jagorancin Alhassan Ado Doguwa.
A cikin wata wasika da Emefiele ya aike wa zauren majalisar a wannan Alhamis ya bayyana cewa, ba zai samu damar halartar zaman ba.
Read Also:
Majalisar Wakilan ta gayyace shi domin yi mata bayani game da gazawar bankin na CBN wajen wadata sassan Najeriya da sabbin takarddun kudin Naira a daidai lokacin da wa’adin ranar 31 ga watan nan na Janairiu na daina amfani da tsoffin kudin ya kusan cika.
.
Da dama daga cikin ‘yan Najeriya na farbagar halin da za su tsinci kansu a ciki muddin wa’adin daina amfani da tsoffin Naira ya kawo karshe ba tare da sauya musu da sabbin ba, lamarin da masana tattalin arziki ke cewa, zai jefa miliyoyin mutanen kasar cikin talauci.
Gwamnatin tarayya ta ce, ba za ta tsawaita wa’adin ba kamar yadda ‘yan kasar suka bukata, yayin da ‘yan kasuwa ke kokawa kan rashin musanya musu tsohuwar Nairar da sabuwa a bankunan kasar.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 7 hours 56 minutes 18 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 9 hours 37 minutes 43 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com