Home General Buhari ya kaddamar da Tashar Tsandauri ta Dala Inland Dry Port

Buhari ya kaddamar da Tashar Tsandauri ta Dala Inland Dry Port

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iso jihar kano domin bude wasu muhimman aiyuka da gwamnatin tarayya da ta Kano suka gudanar.

Buhari ya isa tashar tsandauri ta Dala dake Zawaciki a karamar hukumar kumbotso ta Kano da misali karfe goma da mintina 23.
Buhari ya Sami tarba daga Gwamna jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da masu martaba sarakunan Bichi Rano Gaya da Karaye da sauran ministoci da kwamishinoni gwamnatin jihar kano.
 Ya kaddamar da tashar wadda zata baiwa yan kasuwa damar kawo kayan su daga ko Ina a duniya, maimakon yadda a baya sai sun je jihar Legos sun dauko, wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin jihar kano da kasa baki daya.
Yanzu haka Shugaban Kasar da Gwamna Ganduje sun tafi garin Tiga domin bude gidan wuta, wanda gwamnatin jiha kano ta samar daga nan zai je gidan sarki da. sauran wuraren da zai ziyarta ta a yau.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp