Home General Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sakai 41 a Jihar Katsina

Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sakai 41 a Jihar Katsina

Mazauna wasu kauyuka da ke karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina na zaman makoki sakamakon rasa yan uwansu da dama.

Hakan na zuwa ne yayin da wasu yan ta’adda suka kashe a kalla Yansakai 41 tare da raunata 2 yayin wani artabu a dajin Yargoje.

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa Yansakai din sun bi yan ta’addan daji ne da nufin kwato shanu da suka sace.

Jihar Katsina – Wani artabu da aka yi tsakanin yan ta’adda da kungiyar tsaro ta yan sa kai da aka haramta ayyukansu ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 41 a Katsina.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin ta cikin wata  sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Yansakai sun bi sahun yan bindigan ne bayan sun sace shanu Ya ce yan haramtaciyyar kungiyar ta Yansakai daga kauyuka 11 a karamar hukumar Bakori, sun hadu sun bi sahun yan ta’addan da nufin karbo shanu da suka sace.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce mambobin haramtaciyar kungiyar sun bi sahun yan ta’addan sun gano su a wani wuri a dajin Yargoje inda yan ta’addan suka musu harin kwaton bauna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp