Hukumar NDLEA ta Kama Mai Juna Biyu Kan Kokarin Safarar Miyagun Kwayoyi

Wata mata mai dauke da juna biyu ta fada komar NDLEA bayan da tayi kokarin safarar miyagun kwayoyi.

Matar wanda ta kunshe wiwi a cikin kananan rediyo guda biyu, tayi nufin aika kayan Dubai kafin ta shiga hannu.

Jami’an NDLEA na ci gaba da yunkuri wajen dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi kamar yadda kakin su na Lagos ya bayyana.

Legas – Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke sansanin fita da kaya ta NAHCO shiyyar filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad, da ke Ikeja, Lagos, sun kama wata mata mai juna biyu, Mrs Sylvester Gloria Onome, ranar Litin, 30 ga watan Janairu, 2023, saboda samun ta da miyagun kwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ranar Lahadi a Abuja ya ce an kama matar da giram 800 na wiwi da aka boye a cikin kananan rediyo da za a tura Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, rahoton Vanguard.

Duk a ranar, Hukumar NDLEA ta kuma dakatar da wasu kayan da aka tura jamhuriyyar Congo, Kinshasa, dauke da kwalabe 111 da mayukan shafawa da aka boye kilo 24.50 na ephedrine, wani sinadari da ake amfani da shi wajen hada methamphetamine

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1240 days 1 hour 53 minutes 41 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1222 days 3 hours 35 minutes 6 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com