Kotun Ƙolin Najeriya ta gargaɗi masu sukarta game da hukuncin da ta yanke da ya bai wa shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmada Lawan da Sanata Godswill Akpabio, nasara a matsayin halastattun ‘yan takarar sanata a jam’iyyar APC.
Kotun Ƙolin dai ta umarci hukumar zaɓen ƙasar INEC da ta amince da sunayen sanatocin biyu a matsayin ‘yan takarar kujerun sanata a jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar a babban zaɓen ƙasar da ke tafe ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Read Also:
Tun bayan wannan hukunci ne dai mutane ke cigaba da sukar kotun da ɓangaren shari’ar ƙasar, ciki har da fitaccen marubucin nan Farfesa Faroq Kperogi, ɗan Najeriya mazaunin Amurka.
A wata sanarwa da Kotun Ƙolin ƙasar ta fitar da hannun daraktan yaɗa labaranta Dakta Festus Akande ta gargaɗi masu sukar kotun da su guji aikata hakan.
Kotun ta jadadda cewa ”Mu ba ‘yan siyasa ba ne, kuma ba za mu zama ‘yan siyasa ba, dan haka bai kamata a ɗauke mu a wannan matsayi ba. Babu ra’ayin wani mutum da zai fi ra’ayin kowa. Najeriya gaba take da kowa- da-kowa, dan haka waɗannan kalamai sun isa haka”.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1240 days 3 hours 52 minutes 42 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1222 days 5 hours 34 minutes 7 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com