Shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki a dambarwar diflomasiyya da ke tsakanin Najeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), wadda ta kai ga ƙasar ta Gabas ta Tsakiya ta dakatar da bai wa ‘yan Najeriya takardar izinin shiga cikinta, wato biza.
A wata tattaunawa ta waya da Shugaba Buhari ya yi ranar Litinin da takwaransa na Daular, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, wanda kuma shi ne Sarkin Abu Dhabi ya yi maganar neman ɗage dakatarwar.
Read Also:
Tattaunawar da Shugaba Buharin ya yi da Sheikh Al Nathan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban na Najeriya Mallam Garba Shehu, ya fitar yau Talata
A watan Oktoba na shekarar da ta wuce ne 2022 hukumomin Daular suka dauki matakin dakatar da bai wa ‘yan Najeriya bizar, sai wadanda suke da fasfo na manya wato na diflomasiyya kawai.
Duk da cewa hukumomin ƙasar ta Larabawa ba su bayyana dalilinsu na ɗaukar matakin ba, wasu na danganta shi ga rashin ɗa’a da bin doka da oda da wasu ‘yan Najeriyar da ke zaune ko aiki a can suke yi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1246 days 3 hours 54 minutes 49 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1228 days 5 hours 36 minutes 14 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com