CBN yace suna nan akan bakar su na daina karbar Tsoffin Kudi

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce har yanzu suna kan bakarsu na wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu game da daina karbar tsoffin takardun kudi a fadin kasar.

Emefiele na bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga jami’an diflomasiyya na kasashen duniya a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya da ke Abuja, babban birnin kasar.

“An fara samun sassaucin karancin kudin da ake fama da shi a sassan kasar, sakamakon karba da ake yi a banki wanda hakan ke nufin sabbin takardun kudi sun wadata, saboda haka babu dalilin kara wa’adin ci gaba da karbar tsoffin takardun kudi,” in ji Emefiele.

Wannan matakin dai ya kara jefa al’ummar Najeriya cikin rudani, bayan da kotun kolin kasar ta wa’adin zuwa ranar 15 ga watan Fabrairu, kafin ta yanke hukunci na karshe. Sai dai Gwamnan Babban Bankin na wannan jawabi daidai lokacin da wasu bankuna a kasar suka daina karbar tsofaffin kudin a hannun Al’umma wanda hakan ke alamta cewa Al’umma kasar.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1255 days 7 hours 58 minutes 46 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1237 days 9 hours 40 minutes 11 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com