Home General NDLEA ta kama muggan ƙwayoyin da aka yi niyyar kai su Turai

NDLEA ta kama muggan ƙwayoyin da aka yi niyyar kai su Turai

Hukumar hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce ta ƙwace hodar ibilis da tabar wiwi, da wasu muggan ƙwayoyi da aka yi niyyar fitar da su zuwa Turai da wasu sassan na duniya.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta ce ta kama hodar ibilis da nauyinta ya kai kilogram 58, da kuma tabar wiwi a filayen jiragen saman Abuja da Legas da kuma wasu wurare a ƙasar.

Sanarwar ta ce jami’an hukumar sun kama wasu ‘yan kasuwa uku da take zargi da hannu a yankin Ojo da ke Legas

Haka kuma hukumar ta ce ta kwato ƙwayoyin Tramadol miliyan 2,684,900 da wasu magunguna a lokacin samamen da ta gabatar a makon da ya gabata a faɗin ƙasar.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp