Akalla sojojin Burkina Faso 51 ne aka tabbatar da cewa sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunuka, sakamakon wani harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai wa dakaru a yankin Sahel kamar dai yadda rundunar sojin kasar ta sanar a wannan litinin.
Wannan lamari dai ya faru ne a ranar juma’a da ta gabata, inda da farko aka ruwaito cewa sojoji 8 ne suka rasa rayukansu, kafin wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar a wannan litinin ta bayyana gano karin gawarwakin wasu 43 a inda lamarin ya faru.
Read Also:
Sanarwar ta ci gaba da cewa an kashe ‘yan ta’adda akalla 167, bayan da rundunar sojin saman kasar ta kai daukin gaggawa domin taimaka wa dakarunta.
Hakazalika sanarwar ta ce an lalata ko kuma kwace makamai da kuma babura masu tarin yawa wadanda ‘yan ta’addan ke amfani da su a gumurzun da aka yi tsakanin garuruwan Deou da Oursi da ke yakin na Sahel.
Burkina Faso dai ta jima tana fama da hare-haren masus ikirarin jihadi musamman a yankin Arewaci da kuma gabashin kasar, yayin da wannan barazana ke ci gaba da yaduwa hatta a wasu yankuna da ke kudancin kasar iyaka da Jamhuriyar Benin, Togo da kuma Ghana.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 13 hours 22 minutes 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 15 hours 3 minutes 53 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com