Amurka ta bayyana Nijeriya matsayin kasa mai muhimmanci ga duniya baki daya, ga da bukatar yan kasar su gudanar da zabe cikin lumana.
Wannan na Wani sako na musamman da manyan jami’an gwamnatin kasar suka nada ta bidiyo mai tsawon mintina 58 suka kuma aikewa jama’ar kasar,
Sakon da ya janyo hankalin ‘yan siyasa da kuma jama’a baki daya da su bada gudumawa wajen ganin anyi zabe mai inganci a karshen wannan mako.
Cikin wadanda suka gabatar da sakonninsu a bidiyon sun hada da Sakataren harkokin waje Anthony Blinken da Babbar jami’ar USAID Samantha Power da Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield.
Read Also:
Sakon ya bayyana cewar ‘yan Najeriya sun sake samun wata dama na bayyana ra’ayoyinsu da kuma zabin shugaban da suke bukata ta hanyar zabe saboda muhimmancin kuri’un su.
Blinken yace muhimmancin wannan zaben da zai gudana a karshen wannan mako ba wai ya tsaya kawai ga Najeriya bane, har ma da duniya baki daya.
Wakilan gwamnatin sun jaddada cewar Amurka bata goyan bayan wani ‘dan takara guda, amma kuma tana goyan bayan shirin wanda zai baiwa jama’ar kasar zabin abinda suke so ta hanyar lumana.
Sakon yace samun gudanar da karbabben zaben cikin kwanciyar hankali zai taimaka wajen samun dorewar zaman lafiya a duniya baki daya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1245 days 16 hours 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1227 days 17 hours 41 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com