Yayin da ya rage ƙasa da awa 48 a fara gudanar da zaɓen shugaban Najeriya na 2023, hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC na ci gaba da bayyana shirye-shiryenta na gudanar da zaɓen.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, inda tace zuwa yanzu mutanen da suka karɓi katinsu na zaɓe na din-din-din, sun kai miliyan 87,209,007.
Read Also:
Ta kuma ce akwai mutum miliyan 6,259,229 su ne adadin waɗan da ba su karɓi katin nasu ba ya zuwa yanzu.
Jumillar adadin waɗanda suka yi katin zaɓen a Najeriya ya kai 93,468,236.
Cikin jadawalin ta bayyana yawan katunan da kowacce jiha ta karba da wanda ba a karba ba da kuma kashi nawa ta karba cikin 100.
Matsalolin da Nijeriya ke fama dasu kamada daga tsaro zuwa tattalin arziki ya sanya ana kallon zaben 2023 dake tafe matsayin mai cike da kalubale
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 14 hours 52 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 16 hours 33 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com