Kwamitin karkashin Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar, inda ya ce tun bayan gudanar da zaɓe ranar Asabar sun sanya ido, inda ya ce duk da cewa an samu kura-kurai da ‘yan matsaloli, amma zaɓukan sun gudana lami lafiya.
Wannan kira na kwamitin zaman lafiya na zuwa ne bayan da manyan jam’iyyun adawa a zaben shugaban Najeriya ke kokawa kan ingancin sa.
Ya ce a daidai lokacin da hankali ya karkata wajen jin sakamakon zaɓen, suna kira ga hukumar zaɓe da ta saurari korafe-korafen mutane wajen gudanar da bincike kan zargin tafka maguɗi da tabbatar da an yi wa dukkan waɗanda suka fita suka yi zaɓe adalci.
Kwamitin ya ce ya samu rahotannin da suka nuna cewa an musguna wa wasu masu zaɓe a sassan ƙasar da dama ta hanyar tayar da rikici da hargitsa wajen kaɗa kuri’a da sayen kuri’a da kuma matsalolin da aka fuskanta da na’urar tantance masu zabe.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce yana kira ga dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa da cewa su ne za su ɗauki alhakin duk abin da masu magana da su suka faɗa, inda ya ce su guji furta kalaman da za su tayar da rikici ganin cewa sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar yin zaɓe lafiya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1244 days 13 hours 8 minutes 9 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1226 days 14 hours 49 minutes 34 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com