Home General Jam’iyyun siyasa 7 a jihar Bauchi sun sanya hannu a dokar zaman...

Jam’iyyun siyasa 7 a jihar Bauchi sun sanya hannu a dokar zaman lafiya

‘Yan takarar gwamna na jam’iyyun siyasa 7 a jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Nijeriya sun sanya hannun a yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben gwamnoni dake tafe ranar asabar a jihohin kasar.

Taron sanya hannun ya gudana ne a ranar laraba a dakin taro na shalkwatar rundunar ‘yan sanda dake jihar Bauchi.

‘yan takarar da suka sami halartar taron sanya hannun sun hadar da gwamnan jihar dake neman wa’adi na 2 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, sai halliru Dauda Jika, na jam’iyyar NNPP, sai kuma sadique Abubakar na jam’iyyar APC wanda abokin takarar sa Shehu Musa ya wakilce shi a yayin taron.

Sauran sun hadar da ‘yan takarar jam’iyyun LP, YPP, ZLP da kuma PRP, sai dai  a yayin taron ba’a wakilcin jam’iyyun ADC, AC ba.

Haka kuma an hangi wakilcin rundunar sojin Nijeriya, rundunar tsaro ta DSS, jami’an tsaro na Civil Defence, dakarun hukumar hana fasa Kwauri ta Customs, jami’an NDLEA, jami’an dake lura da shige da fice na NIS, da masu lura da ajiya da gyaran hali da tarbiyya.

Kwamishin ‘yan sanda jihar ya karanta sashe na 125 da na 126 na dokar zabe ta 2022 da aka yiwa gyaran fuska matsayin wukar kugun da yayi amfani da ita wajen gargadin ‘yan takarar domin bin doka da Oda a yayin zaben.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp