Home DUNIYA UNICEF ta koka da karuwar matan da basa samun wadataccen abinci mai...

UNICEF ta koka da karuwar matan da basa samun wadataccen abinci mai gina jiki

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya koka da karuwar matan da basa samun wadataccen abinci mai gina ciki musamman masu juna biyu da masu shayarwa.

UNICEF cikin wani rahoto da ya fitar ya ce an samu karuwar matsalar da akalla kashi 25 cikin kasashe 13 galibinsu a Afrika da Asiya, tana mai gargadin cewa idan har ba a dauki matakan magance matsalar ba, ko shakka babu za a samu karuwar haifar jarirai masu ciwon yunwa ko kuma Tamow.

Alkaluman da ke kunshe a rahoton na UNICEF ya nuna cewa adadin mata masu juna biyu da masu shayarwa wadanda basa samun abinci mai gina jiki ya karu daga mutum miliyan 5.5 a shekarar 2020 zuwa miliyan 6 da dubu dari 9 a bana.

Rahoton na UNICEF ya alakanta koma bayan da yadda yakin Rasha a Ukraine ya haddasa yunwa musamman a kasashen da suka dogara da ketare ta fannin abinci.

Rahoton na UNICEF ya ce galibin kasashen da wannan matsala ta fi tsananta na sahun wadanda ko dai su ke fama da rikici ko kuma wadanda ‘yan tawaye ko ‘yan ta’adda ke barazana ga tsaronsu.

Cikin jerin kasashen da rahoton ya bayyana a matsayin kan gaba da ke fama da wannan matsala ta yawaitar matan da basa samun abinci mai gina jiki akwai Afghanistan a kan gaba kana Burkina Faso da Chadi da Habasha sannan Kenya da Mali da Nijar sai Najeriya da Somalia tukuna Sudan da Sudan ta kudu sai kuma Yemen.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp