Wani sabon harin mayakan tayar da kayar baya na ADF a gabashin jamhuriyyar damukradiyyar Congo yayi sanadiyyar mutuwar mutane 40 kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Shugaban wata kungiyar Al’umma a kauyen mukondi ne ya tabbata da faruwar lamarin inda yace mayakan sun hallaka mutanen ne da wukake.
Read Also:
Kungiyar ‘yan tawayen ADF ta samo asali ne daga kasar Uganda wadda ta fara gudanar da ayyukan ta a gabashin Congo a tsakiyar shekarun 1990, wanda aka ce mafi yawa cikin ‘ya’yan kungiyar musulmai ne dake kisan gilla ga fararen hula.
A shekara 2021 ma an alakanta hare-hare da aka kai kasar Uganda kuma aka kaddamar da wani farmaki na hadin gwiwa tsakanin sojojin congo da na Uganda domin farautar mayakan a Arewacin Kivu da kuma lardin Ituri dake makwabtaka da su.
Ko a makon daya gaba ta kasar Amurka ta sanya tukuicin dala miliyan biyar ga wanda ya bayar da bayanan yadda za’a kama shuganban kungiyar.