• Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Search
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.
PRNIGERIA PRNigeria Hausa
PRNIGERIA PRNIGERIA
  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
Home SIYASA Adamawa: Ayyana Zaɓen Gwamna a Matsayin Wanda bai Kammala ba shi ne...
  • SIYASA

Adamawa: Ayyana Zaɓen Gwamna a Matsayin Wanda bai Kammala ba shi ne Daidai – Binani

By
By Prnigeria
-
March 25, 2023
Binani
Arewa Award

Adamawa: Ayyana Zaɓen Gwamna a Matsayin Wanda bai Kammala ba shi ne Daidai – Binani

 

‘Yar takarar kujerar gwaman jihar Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta bayyana goyon bayanta kan matakin hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka na bayyana zaɓen gwaman jihar a matsayin wanda bai kammala ba.

Yayin da ta bayyana a cikin shirin ‘Politics Today’ na gidan talbijin ɗin Channels Tv, Sanata Aishatu Binani ta yi maraba da matakin, inda ta yi zargin cewa an aikata kura-kurai da rikice-rikice a wasu ƙananan hukumomin jihar.

Read Also:

  • NDLEA ta kama Ba’indiye da wasu mutane da ƙwaya ta naira biliyan uku a Legas
  • Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi
  • Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Muhammadu Mele na jami’ar Maiduguri ne ya ayyana sakamakon zaɓen gwaman jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwaman jihar mai ci Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ke neman wa’adin mulkin jihar karo na biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 421,524, yayin da ita kuma Sanata Binani ta jam’iyyar APC ke da yawan ƙuri’u 390,275.

Jami’in zaɓen ya bayyana cewa ba a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 69 a faɗin jihar ba, kuma adadin katunan zaɓen da aka karɓa a duka rumfunan sun kai 37,016, wanda kuma adadinsu ya zarta tazarar ƙuri’u 31,249 da ke tsakanin ‘yan takarar biyu.

Sanata Aishatu ta ce ”matsayina game da matakin shi ne jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar ya yi daidai da ya bayyana sakamakon zaɓen jihar a matsayin wanda bai kammala ba’

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Previous articleZambar N2.2bn: EFCC ta Sake Gurfanar da ɗan Tsohon Shugaban PDP
Next articleKotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar da PDP ta shigar kan Tinubu da Shettima
By Prnigeria

RELATED ARTICLESMORE FROM AUTHOR

Ban koma jam’iyyar APC ba – Namadi Sambo

Barau ya nada shugaban kungiyar zago akida na Kano mukami

Nima ɗan ƙungiyar Zago Akida ne -Sanata Barau

Gwamnoni ku dauki aniyar hidimtawa Al’umma – buhari

Atiku ya yi martani kan kalaman Akume ga ‘yan Arewa

An sake zaɓar Okonjo-Iweala shugabar WTO a wa’adi na biyu

Dalilin Ndume na sa alamar tambaya kan gaggawar amincewa da ƙudurin haraji na Tinubu

Yahaya Bello ya musanta zargin rashawa a gaban kotu

Hukumar EFCC ta ce ta yi nasarar kama Yahaya Bello

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen jihar Ondo

Kotu ta ɗage shari’ar EFCC da Yahaya Bello zuwa Janairu

Recent Posts

  • NDLEA ta kama Ba’indiye da wasu mutane da ƙwaya ta naira biliyan uku a Legas
  • Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi
  • Kotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15
  • Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin Mauludi
  • Hukumar DSS ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar Ansaru

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1551 days 14 hours 12 minutes 30 seconds,



Baptist School Students, Kaduna
1533 days 15 hours 53 minutes 55 seconds

Report By: prnigeria.com/hausa

Book on Sales: Boko Haram Media War: An Encounter with the Spymaster

boko haram

Click Here:To Order Now!

  • Gida
  • DUNIYA
  • Labarai
  • SIYASA
  • TARIHI
  • Taska
  • WASANNI
© 2020 PRNigeria. All Rights Reserved.
Latest News
NDLEA ta kama Ba'indiye da wasu mutane da ƙwaya ta naira biliyan uku a LegasLikitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗiKotu ta yanke wa kwamandan Ansaru hukunci ɗaurin shekaru 15Gwamnatin Kano ta bayar da hutun bikin MauludiHukumar DSS ta yi holen manyan kwamandojin ƙungiyar AnsaruNUPENG ta cimma matsaya da kamfanin DangoteƘungiyar ƙwadago ta TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki a NajeriyaEl-Rufa'i ya shigar da ƙorafi kan zargin ƴansanda da cin zarafi'Yan sandan Jigawa sun kama Dilolin kwaya a jiharKofa ya sanar da ficewarsa da ga NNPPBurkina Faso ta amince da dokar haramta neman maza a faɗin ƙasarAn bayyana jihohin arewacin Najeriya da za su iya fuskantar ambaliya a watan SatumbaGwamnatin Najeriya ta yi maraba da ɗaure Simon Ekpa a FinlandAtiku ya nemi a soke sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin RiversAn yanke wa ɗan Najeriya Simon Ekpa hukuncin ɗaurin shekara 6 a Finland
X whatsapp