Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP ya amince da naɗin Ambasada Umar Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa.
Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar bayan ganawar gaggawa da kwamitin gudanarwar PDP na ƙasa ya yi ranar Talata, ta ce ta ɗauki matakin ne don yin biyayya ga hukuncin babbar kotun jihar Binuwai.
A ranar Litinin ne kotu a Binuwai ta haramta wa Ayu ci gaba da gabatar da kansa a matsayin shugaban PDP, har sai ta saurari ƙarar da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka shigar gabanta.
Da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron a shalkwatar PDP ta ƙasa, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ya ce sun ɗauki matakin naɗa Damagum ne domin bin umarnin tsarin mulkin PDP.
“Bayan nazari a kan hukuncin kotun da kuma la’akari da sashe na 45 (2) na tsarin mulkin PDP, kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya amince da naɗa mataimakin shugaban PDP mai kula da shiyyar arewa, Amb. Umar Ililya Damagum a matsayin sabon shugaban riƙo na jam’iyyar”.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 10 hours 53 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 34 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com