Home SIYASA Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida fatan alheri a mulkin Kano

Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida fatan alheri a mulkin Kano

Mataimakin gwamnan Kano kuma ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar, Nasir Yusuf Gawuna ya yi wa zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf addu’ar samun nasara a mulkinsa tare da yi wa kansa da magoya bayan jam’iyyar APC fatan ɗaukar kaddara.

Gawuna ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙon murya da aka naɗa, wadda aka rabawa manema labarai a jihar kano.

Matakin na zuwa ne jim kaɗan bayan Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta bai wa Abba Gida-Gida takardar shaidar cin zaɓen gwamna a ranar Laraba.

A cikin saƙon, Nasir Gawuna ya ce “shi (Abba) wanda Allah Ya bai wa, Allah Ya sa ya zama shugaba nagari, mai adalci ga kowa.”

Ya ƙara da cewa “Mu kuma Allah Ya sa mu zama masu biyayya ga shugabanci da kuma bin doka.”

Gawuna ya buƙaci magoya bayansa su ƙara haƙuri tare da addu’ar ɗaukan kadara a rashin nasarar da jam’iyyar ta yi a zaɓen gwamna na shekarar 2023.

A ranar 20 ga watan Mayu ne, INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano bayan zaɓen da aka yi ranar 18 ga watan na Mayu.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan Kano Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya ce Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.

Sai dai jam’iyyar APC ta ce ba ta yarda da sakamakon ba, kuma ta buƙaci INEC ta sake nazari kan zaɓen.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp