Home DUNIYA Fada ya kaure tsakanin sojojin Sudan da runduna ta musamman

Fada ya kaure tsakanin sojojin Sudan da runduna ta musamman

An ji karar fashe fashe a babban birnin Sudan, Khartoum a yau Asabar, sakamakon rikicin da ya kaure tsakanin dakaru na musamman da ke gadin fadar shugaban kasar da sojoji, kwanaki bayan da rundunar sojin kasar ta yi kashedin cewa kasar ta shiga wani matsayi mai hatsari.

Rikicin ya  barke ne  bayan da aka shafe makwanni ana zaman tankiya tsakanin jagoran gwamnatin sojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa, kuma kwamandan runduna ta musamman na kasar, Hamdan Daglo.

Ganau sun ruwaito cewa an yi arangama, inda aka ji karar fashe fashe a kusa da ofishin runduna ta musamman, wato RSF.

Runduna ta musamman ta ce dakarunta sun karbe iko da filin jirgin sama na birnin Khartoum a halin da ake ciki, bayan da shaidu suka ce sun hango motoci cike da mayaka na shiga cikin harabar filin jirgin saman.

sun ruwaito cewa sun jiyo karar  harbe harbe a kusa da filin jirgin saman, da kuma kusa da gidan Burhan a arewacin birnin Khartoum.

An hango fararen hula suna ta tserewa don tsira da rayukansu.

Bangarorin biyu dai na zargin jina da  tada rikicin.

Jagoran mulkin sojin Sudan, Burhan da mataimakainsa suna cikin rashin jituwa ne a kan tattaunawar yarjejeniyar mika mulki ga farar hula tare da karshen rikicin da ya kunno kai tun bayan juyin mulkin shekarar 2021.

Runduna ta musamman ta RSF da aka kirkiro  a shekarar 2013 ta sao asali ne daga kungiyaar ‘yaan tsagerar Janjaweed, wadda tsohon shugaban kasar, Omar al-Bashir ya yi amafani da ita wajen muzgunawa ‘yan tsirarun kabilu wadanda ba Larabawa ba a yankin yammacin Darfur, lamarin da yanzu ya janyo masa tuhumar aikata laifukan yaki.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp