Sama da Mutane dubu 3 sun rasa muhallin su a kasar Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da 400 suka mutu ya zuwa wannan lokaci a rikicin kasar Sudan, yayin da sama da 3,500 suka samu raunuka daban daban.

Majlisar ta kuma kara da cewa daga cikin mutanen da suka mutu akwai yara kanana guda 9, bayan sama da 50 da suka jikkata.

Mai Magana da yawun hukumar lafiya ta duniya Margareth Harris ce ta gabatar da wadannan alkaluma masu tada hankali, sakamakon rahotannin da suke tattarawa daga hannun hukumomin lafiyar Sudan.

Harris ta ce yanzu haka asibitocin kula da lafiyar jama’a guda 20 sun daina aiki a Sudan saboda tashin hankalin, yayin da wasukarin 12 ke fuskantar barazanar dakatar da aikace aikacensu, wanda ake ganin na iya haifar da karin illa ga jama’a.

Shima mai Magana da yawun Hukumar da ke kula da kananan yara ta Majalisar wato UNICEF, James Elder ya ce rufe asibitocin ba wai kawai zai shafi wadanda suka samu raunuka sakamakon wannan tashin hankalin bane, har ma da marasa lafiyar da ke bukatar kulawa.

Elder ya ce dama kasar Sudan na daya daga cikin kasashen da ke da yawan yara masu fama da tamowa, kuma ganin yadda wannan rikici yayi kamari, ana iya samun karin yara kusan dubu 50 da za su fuskanci wannan matsala.

Rahotanni sun ce har a yau da juma’a ke bikin Sallar Idi, ana ta yin barín wuta tsakanin bangarorin biyu da ke kokawar mulki a cikin kasar.

Kungiyar likitoci ta kasa ta ce daren jiya anyi ta jin karar fashewar bama bamai da kuma amon makaman atilare a birnin Khartoum, yayin da sojojin gwamnati da na kungiyar RSF ke musayar wuta da bindigogi a tsakaninsu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres tare da Sakataren harkokin wajen Amurka Antonio Blinken sun bukaci tsagaita wuta na tsawon kwanaki 3 domin bai wa jama’a damar gudanar da bukukuwan Sallah.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 13 minutes 27 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 54 minutes 52 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com