Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu 800 ne ake sa ran za su tsere daga Sudan sakamakon kazamin rikicin da ake yi tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun Kai Daukin Gaggawa na RSF.
Read Also:
Wani babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya, Raouf Mazou ne ya bayyana haka a Geneva, ina yake cewa idan ba a warware wannan rikici da wuri ba, za a ci gaba da samun dimbim mutanen da ke arcewa daga Sudan don neman mafaka da agaji.
Saboda haka ya ce a tattaunawar da suka yi da hukumomin da wannan lamari zai shafa, sun cimma matsayar shirya wa mutane dubu 815 da ake sa ran za su iya arcewa zuwa kasashe 7 da ke makwaftaka da Sudan.
Wannan hasashe da aka yi, in ji Mazou ya hada da kimanin ‘yan kasar Sudan dubu 580 da kuma wadanda ke gudun hijira a halin yanzu daga Sudan ta Kudu da wasu wuraren.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 58 minutes 44 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 40 minutes 9 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com