Home SIYASA yadda Tinubuya gana da Kwankwaso a kasar Faransa

yadda Tinubuya gana da Kwankwaso a kasar Faransa

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wata ganawa da zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a birnin Paris.

Bayanai sun nuna cewa mutanen biyu sun shafe sa’o’i da dama suna tattaunawar.

Kwankwaso, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Kano ya zo na huɗu a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023, inda ya samu ƙuri’u 1,496,687.

Duk da cewa babu cikakken bayani kan abin da tattaunawar ta ƙunsa, amma ana ganin cewa ba za ta rasa nasaba da shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnati da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu ba.

Bola Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake wa kallon ƙwararru a siyasar Najeriya, har yanzu bai yi bayani dalla-dalla kan yadda gwamnatinsa za ta kasance ba.

A halin da ake ciki, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bola Tinubu na ƙoƙari ne wajen ganin ya shirya yadda zai karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayu.

A ranar Laraba 10 ga watan Mayu ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai tafi wata ziyarar aiki a ƙasashen Turai.

PRnigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp