Home SIYASA Gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin wasu hukumomi da ma’aikatun gwamnati.

Wannan na kunshe ta cikin wata Sanarwa da babban sakataren yada labaran gwaman, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa PRNigeria.

Wadanda aka nada din sune kamar haka.

1. Injiniya Ado Ibrahim Umar, Manajan Darakta na Kamfanin Wutar Lantarki na Kano (KHEDCO)

2. Alh. Auwalu Mukhtar Bichi, Manajan Daraktan Kamfanin Zuba Jari na kano.

3. Dr. Farouq Kurawa, Manajan Daraktan Hukumar KNARDA.

kafin ba shi wannan mukami , Dakta Kurawa shi ne Babban Sakataren gwamnan Kano wato (PPS) .

4. Dr. Tukur Dayyabu Minjibir, Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Taki na Kano (KASCO).

5. Hussain Sarki Aliyu Madobi, Manajan Darakta na Cigaban aiyuka a Kano wato (SKP)

6. Sadiq Kura Muhammad, Manajan Darakta na gidan Zoo Kano (ZGK)

7. Injiniya Sani Bala, Manajan Daraktan Hukumar samar da wutar Lantarki a Karkara (REB)

8. Shamwilu Gezawa, hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta jihar Kano (RUWASA)

9. Alh. Tukur Bala Sagagi, Manajan Darakta na hukumar yawon bude ido ta jihar Kano

10. Alh. Yahaya Muhammad Idris Manajan Daraktan Kamfanin dab’i na Jihar Kano.

11. Adamu Yahaya, Mataimakin Manajin Darakta (DMD), Kamfanin dab’i na Kano

12. Abba El-mustapha, Sakataren zartarwa na Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano

13. Dr. Muhammad S. Khalil, Babban Sakatare na Hukumar Kula da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano (KN-WECCMA).

14. Dr. Dahir M. Hashim, Kodineta na Hukumar Kula da Sauyin yanayi ta Jihar Kano (KN-WECCMA).

Sanarwar na umartar Dukkanin wadanda aka nada dasu karbi ragamar aikin da aka dora musu nan take

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp