Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago, yace hukumar sa zata yi amfani da sashin dokar ma’aikatar wajen tursasawa tare da magance dabi’ar zubar da shara da tsakar dare a wuraren da basu kamata ba a jihar Kano.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai yayin da ma’aikatan hukumar suke tsaka da aikin kwashe sharar dake fagge ‘yan Alluna.
Read Also:
Dan zago yace abin takaici ne yadda wasu suke bin tsakar dare suna jibge sharar akan titunan jihar nan da wuraren da basu dace ba musamman wuraren da aka kwashe sharar tun da farko.
A bayanansu tunda farko mazauna kasuwar ta ‘yan fagge ‘yan Alluna sun yaba da yadda aikin kwashe sharar yake gudana a fadin jihar nan Koda dai wasu daga cikin su sun bayyana cewa kamata gwamnati ta gudanar da aikin tuntuni.
Daga cikin wuraren da hukumar kwashe sharar tayi aiki a yau sun hada da fagge ‘yan Alluna, karkashin gadar kasuwar Bata da New Road dake Unguwar Sabon Gari.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 34 minutes 32 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 15 minutes 57 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com