Matakin Soji zai zama na karshe kan sojojin Nijar – Manyan Hafsoshin ECOWAS

Manyan hafsoshin tsaron ƙungiyar Ecowas za su samar da mafita idan dukkan hanyoyin da aka bi a siyasance ba su yi tasiri ba bayan juyin mulki a Nijar.

Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya JanarTukur Gusau ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron da suka gudanar, in da yace matakin soji zai zamo na karshe.

“Matakin soji zai zama na ƙarshe da za a ɗaukar kan dakarun sojojin da suka yi Juyin Mulki a kasar, ”

Manyan hafsoshin tsaron ƙungiyar ta raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma na tattaunawa a Abuja daga yau Laraba zuwa Juma’a domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen shawo kan sojojin da suka yi juyin mulkin, inda aka hamɓarrar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a makon da ya gabata.

Manyan hafsoshin tsaron Ghana, da Najeriya, da Benin, da Togo, da Saliyo, da Laberiya, da Gambiya, da Cote D’Ivoire, da Cape Verde ne ke halartar taron.

Sai dai takwarorinsu na Mali, da Nijar, da Guinea Bissau, da Burkina Faso, da Guinea ba su halarta ba sakamakon dakatar da su da Ecowas ta yi daga ƙungiyar saboda juyin mulkin da suka jagoranta a ƙasashensu.

Manyan hafsoshin tsaron za su gabatar da matakin da suka cimma ga shugaban ƙungiyar Bola Tinubu a ranar Juma’a.

Daga nan ne shugaban ƙungiyar zai yanke shawara kan mataki na gaba da za a ɗauka kan sojojin ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya ayyana kan sa a matsayin shugaban Nijar.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 20 minutes 39 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 2 minutes 4 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com