Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce Amurka za ta ci gaba da bayar da taimakon kayan agaji da tallafin abinci ga Jamhuriyar Nijar.
To sai dai Mista Blinken ya ce Amurka za ta dakatar da wasu tallafin da za su taimaka wa ƙasar da ke yammacin Afirka.
Ya ce Amurka za ta ci gaba da samar da tsaro don kare jami’anta da ke ƙasar.
Read Also:
Kalaman Mista Blinken na zuwa ne a daidai lokacin ƙasashen ƙungiyar Ecowas suka amince da amfani da ƙarfin soji a Nijar ɗin, matuƙar sojojin ba su mayar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki ba.
Tuni dai Nijar din ta sanar da janye jakadunta da ke wasu ƙasashen duniya ciki har da Amurka da faransa da kuma Najeriya.
A ranar Juma’a ne dai Najeriya ta sanar da rufe kan iyakokin ƙasar da Jamhuriyar ta Nijar, bayan katse wutar lantarki da take bai wa ƙasar, a wani mataki na tilasta wa sojojin mayar da Bazoum kan mulki.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 41 minutes 41 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 23 minutes 6 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com