ECOWAS na shirin Lashe amai kan Jamhuriyar Nijar

Alamu na nuna cewa kungiyar ECOWAS na shirin janye barazanar amfani da karfin soji domin mayar da zababiyar gwamnatin a Jamhuriyar Nijar.

Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da kungiyar da mambobinta a birnin tarayyar Nijeriya aa batun juyin mulkin kasar.

A yayin taron kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, ta ce za ta ci gaba tintibar sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar a yunkurin da take na warware matsalar.

Yayin bude taro na musammman da shugabannin kungiyar a Abuja, shugaban ECOWAS Bola Ahmed Tinubu da ke jagorancin taron ya bayyana taron na yau a matsayin mai matukar muhimmanci wajen ci gaba da dorewar yankin a matsayin dunkulalle wanda zai ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma ci gaban Al’umma.

Shugaban ya ce taronsu na yau zai bada damar cikakken nazari kan ci gaban da aka samu da kuma matsalolin da aka fuskanta tun bayan taron farko da suka yi kan Nijar, domin duba gyaran da ya kamata a yi ko kuma gibin da ya kamata a cike domin gyara lamarin.

Shugaban na ECOWAS ya ce ya zama wajibi a gare su a matsayin shugabanni su fahimci cewar halin da ake ciki a Nijar na zama barazana a gare su, kuma abin da ke iya biyo baya zai shafi yankin baki daya.

Tinubu ya bayyana fatar cewar wannan taro na biyu kan Nijar zai bada damar daukar matakin da ya dace wanda zai taimaka wa yankin baki daya.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 17 minutes 51 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 59 minutes 16 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com