Wasu rahotanni na bayyana cewa Gwamnatin Burkina Faso na shirin aika wa da maƙwabciyarta Nijar hatsi.
Wata sanarwa da ma’aikatar cigaban kasuwanci ta ƙasar ta fitar ranar Juma’a ta ce za a aika wa Nijar ɗin gero da masara da dawa, da dai sauransu.
Yunƙurin na zuwa ne yayin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar takunkuman kasuwanci da na tattalin arziki sakamakon juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a ƙarshen watan Yuli.
Read Also:
Duk da cewa Burkina Faso mamba ce a ECOWAS, ba ta bi umarnin ƙungiyar ba ta raya tattalin arziƙin Afirka ta Yamma saboda ita ma tana cikin takunkumai na juyin mulki.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan kasuwar da ke da sha’awar safarar kayan su tuntuɓi hukumomin da suka dace don isar da kayan zuwa Nijar.
Burkina Faso, da Mali, da Guinea dukkansu mambobin Ecowas da aka dakatar saboda juyin mulki, sun sanar da cewa za su goya wa sojojin mulkin Nijar baya idan ƙungiyar ko kuma dakarun ƙasar waje suka kai musu hari.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 17 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 59 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com