Gwamnatin Nijeriya tace ba za ta yi katsalandan a zaɓukan jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo ba, da ke tafe cikin watan Nuwamba.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a yayin wani taro da shugaban hukumar zaɓen ƙasar, Farfesa Mahmood Yakubu, tare da sauran kwamishinonin zaɓen da sauran masu ruwa da tsaki a sabgar zaɓen.
Ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu na cike da fatan gudanar da sahihin zaɓe a waɗannan jihohi.
“Wannan zaɓuka za su kasance mafiya tsafta fiye da na baya. za su gudana ba tare da rigima ba, za su kasance sahihan zaɓukan da babu katsalandan a cikinsu,” in ji Ribadu.
Ya kuma ce shugaban ƙasa a shirye yake ya goyi bayan hukumar don samun nasarar hakan.
Read Also:
An gudanar da taron ne a ofishinsa a wani ɓangare na tuntuɓa da hukumar ke yi gabanin zaɓukan da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.
Tun da farko INEC ta nuna fargabar tsaro gabanin zaɓukan, a wani taro da ta gudanar da jam’iyyun siyasa.
A nasa ɓangare shugaban INEC, ya bayyana fargabarsa kan tsaron lafiyar masu kaɗa ƙuri’a da tsaron kayayyakin zaɓe masu muhimmanci, tare da tsaron cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.
Ya yi kira ga jami’an tsaro su yi maganin duk wanda ya yi yunƙurin tayar da zaune-tsaye a ranar zaɓen.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 17 hours 56 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 38 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com