Shuwagabannin mulkin sojin Nijar sun kaddamar da wani babban batutun man fetur da zai riƙa tura ɗanyen mai daga ƙasar zuwa Jamhuriyar Benin, mai maƙwabtaka da kasar.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana cewa gidan talabijin na ƙasar ne ya ambata aiki, wanda ke da tsawon kusan kilomita 2,000 da zai bai wa Nijar damar sayar da ɗanyen man fetur da take haƙowa a kasuwannin duniya a karon farko, ta hanyar amfani da mashigar ruwan Seme da ke Benin.
An gudanar da bikin ƙaddamar da aikin cibiyar haƙo man fetur ta Agadem, mai nisan kilomita 1,700 daga Yamai baban birnin ƙasar.
Firaministan Nijar, Ali Mahaman Lamine, ya ce za a yi amfani da kuɗin da aka samu daga cinikin man fetur din “don tabbatar da tsaro da ci gaban ƙasarmu”.
Kan iyakar Nijar da Jamhuriyar Benin ta kasance a rufe sakamakon jerin takunkuman da ƙungiyar Ecowas ta saka wa Nijar bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.
Wakilai daga ma’aikatun makamashin ƙasashen Mali da Burkina Faso – waɗanda ke nuna goyon bayansu ga sabuwar gwamnatin sojin Nijar – sun halarcin bikin ƙaddamar da aikin.
Read Also:
An tsara kammala aikin a shakerar 2022, to amma annobar korona ta haddasa jinkirin aikin, kamar yadda masu gudanar da aikin suka shada wa AFP. Kamfanin man Fetur na Ƙasar China, (CNPC) ne ke aikin haƙo man.
Gwamnatin Nijar ta ce aikin ya laƙume dala biliyan shida, ciki har da dala biliyan huɗu na gina wuraren man, da kuma dala biliyan 2.3 na aikin shimfiɗa bututun man.
Ta ƙara da cewa wannan aiki zai bai wa ƙasar damar ƙara yawan man da take haƙowa zuwa ganga 110,000 a kowace rana, da nufin ƙara shi zuwa 200,000 a kowace rana zuwa shekarar 2026.
Ƙasar Nijar – wadda sojoji suka kifar da gwamnatin farar hula cikin wata Yuli – ta fuskanci jerin zanga-zanga da kiraye-kirayen ficewar sojojin Faransa daga ƙasar.
Ga kuma jerin takunkumai daga ƙungiyar Ecowas, sannan ƙasashen Yamma da dama sun yanke tallafin da suke ba ta.
Bankin duniya ya yi gargaɗin cewa arzikin da ake samu a cikin ƙasar na iya raguwa da kashi 2.3 a wannan shekara matuƙar ba ɗage mata takunkuman ba.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 45 minutes 50 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 27 minutes 15 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com