Home General ‘Yan Sanda Sun tabbatar da harin ‘yan Ta’adda a jihar Adamawa

‘Yan Sanda Sun tabbatar da harin ‘yan Ta’adda a jihar Adamawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da harin ‘yan bindiga a garin Kwapre dake karamar hukumar Hong ta jihar.

kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Sulaiman Ngureje ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar talata a birnin Yola.

inda ya ce lamarin ya auku ne ranar litinin, wato ranar da aka gudanar da bikin kirsimeti, sai dai ya ce har yanzu hukumar na gudanar da bincike bisa aukuwar lamarin.

 ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Babatola Afolabi, ya bayar da umarnin girke jami’an ‘yan sanda domin gudanar da bincike.

ya kuma bukaci al’umma da su tabbatar sun kai rahoton dukkan wani abu da basu yadda da shi ba ga hukumar da kuma dukkan saurarn hukumomin tsaro dake jihar dama kasa baki daya.

haka shima dagacin Dugwaba Mr Simon Buba,  ya tabbatar da faruwar lamarin, in da yace maharan sun hallaka mutane 2,

ya ce ana zargin maharan mambobin kungiyar tayar da kayar baya na  boko haram ne, da suka yiwa garin tsinke kan babura suka kuma yi awon gaba da kayan abinci suka nausa cikin dajin sambisa.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp