Mun Kama ‘Yan dabar da Wani Dan Siyasa ya tura ƙunci da Tsanyawa – CP Gumel.

Rundunar ‘yan Sandan Kano ta tabbatar da kama wasu ‘yan Daba, da ake zargin wani Dan Siyasa ya tura wurin Zaɓen cike gurbi ,na ƙananan Hukumomin ƙunci da Tsanyawa.

Kwamishinan ‘Yan Sandan kano CP. Muhammad Hussaini Gumel ne ya bayyana hakan, Jim kadan da kama gungun matasan a lokacin da suke zagayen yadda Zaɓen cike gurbin yake gudana.

CP Gumel ya ƙara da cewa, tuni ‘Yan daban suka kama sunan ɗan Siyasa me Suna Gwarmai, a matsayin Wanda ya turo su domin su je su tayar da hankali a wurin Zaɓen cike gurbin na Ƙunci da Tsanyawa.

‘Yan Sandan sun kama ‘yan dabar da makamai ne, samfurin Adduna, Gorori, Gariyo, da dai sauran su, a dai-dai lokacin da suke kan hanyar su ta shiga garin Ƙunci.

Gumel yace zasu Binciki Dan Siyasar domin tabbatar da gaskiyar lamarin dama gurfanar dashi a gaban kuliya, matukar zargin yayi ƙarfi a kansa.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1187 days 17 hours 58 minutes 34 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1169 days 19 hours 39 minutes 59 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com