Hukumar da ke sa ido kan kafafen yaɗa labarai a Burkina Faso ta ƙaƙaba dakatarwar mako biyu kan kafar yaɗa labarai na BBC Afrique da Muryar Amurka (VOA) saboda yaɗa rahoton da ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta fitar da ke zargin sojojin ƙasar da cin zarafin farar hula.
Kazalila, hukumar ta dakatar da shafukan intanet na kafofin yaɗa labaran da ƙungiyar Human Rights a cikin ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ruwaito cewa “An umarci BBC da VOA ta hannun wakilansu a Burkina Faso da su gaggauta daina watsa shirye-shirye a dukkanin kafofinsu,”
Read Also:
Hukumar kula da harkokin sadarwa ta sake gargaɗin kafafen yaɗa labarai a ƙasar da su kaucewa yaɗa labarin inda ta yi barazanar ƙaƙaba wa waɗanda suka bijire takunkumi.
A ranar Alhamis ne ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi sojojin Burkina Faso da kashe farar hula aƙalla 223 a arewacin ƙasar ranar 25 ga watan Fabarairu.
A Disamban 2023 ne Burkina Faso ta dakatar da jaridar French daily Le Monde kan zargin nuna son kai a rahotannin da suke yaɗawa.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 32 minutes 58 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 14 minutes 23 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com