An sake dawo da ƙoƙarin bin hanyar diflomasiya domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza, inda ake sa rai wakilai daga Hamas za su ci gaba da tattaunawa a birnin Alƙahira na Masar.
An rawaito wani babban kwamandan Hamas na cewa basu da matsala da sabon daftarin yarjejeniyar da Isra’ila ta gabatar kan tsagaita wuta da sakin fursunoni.
Sai dai babu alamar da ke nuna za a cimma daidaituwar.
Read Also:
Rahotanni na cewa sabbin bayanan yarjejeniyar sun ƙunshi dawo da kwanciyar hankali a Gaza, wanda tabbas za su dadaɗa wa Hamas.
Mataimakin kakakin majalisar Isra’ila Moshe Tur- Paz, ya nuna cewa abin da ya kamata a fi bai wa fifiko a yanzu shi ne dawo da mutanensu da ke garƙame gida.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya je Saudiyya, inda shi ma yake tattaunawa da shugabannin Larabawa kan yiwuwar cimma yarjejeniya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 23 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 17 hours 5 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com