NLC ta bawa Gwamantin Nijeriya Karshen watan Mayu

Kungiyar Kwadago a Najeriya ta bai wa gwamnatin ƙasar nan karshen watan Mayu ta ƙara fito da sabon albashi mafi ƙaranci ga ma’aikatan ƙasar.

Ƙungiyar ta sanar da haka ne yayin bikin murnar ranar ma’aikata ta ƙasa a filin taron Eagle Square da ke Abuja a ranar Laraba.

Shugaban ƙungiyar NLC Joe Ajaero tare da takwaransa na ƙungiyar TUC Festus Osifo sun haɗu kan cewa mafi ƙaranci albashi na naira 30,000 ya yi wa ma’aikatan Najeriya kaɗan duba da yanayin matsi da kuma tsadar rayuwa da ya haɗa da tashin farashin abinci da kuɗin wuta da na sufuri da kuma sauransu.

Sun dage kan naira 615,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci da suke so gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta saka hannu kafin ƙarshen watan Mayun.

Ajaero ya ce, “Kungiyar NLC da ta TUC na jaddada cewa matsawar za a ci gaba da tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi ba tare da mafita ba har zuwa ƙarshen Mayu ba za mu iya ci gaba da ba da haɗin kai ba a ƙasar nan”.

A ɓangaren Osifo kuma ya nemi hukumar kula da wutar lantarki tare da kamfanonin da suke rarraba wutar kan su janye ƙarin kuɗin da su ka yi wa mutane da ke rukunin A waɗanda suka fi samun wuta.

wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin kasar karkashin shugaban Bola Tinubu ta furta batun karin ALbashin ga ma’aikatan kasar da kaso 25 da kuma 35 cikin dari, abinda kungiyoyin kwadagon ke kallon matsayin tufka da warwara.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 12 hours 40 minutes 43 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 22 minutes 8 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com