Kasar Benin ta dauki matakin hana fitar da man da ake fitarwa daga Nijar ta hanyar bututun mai da ya hada rijiyoyin mai na Nijar ta tashar ruwan Cotonou.
Wannan matakin martani ne kai tsaye ga Nijar, wadda ke ci gaba da rufe kan iyakarta da Benin, duk da cewa Ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta ɗage takunkumin da ta kakaba wa gwamnatin Nijar.
Sakamakon haka, ayyukan jiragen ruwa da aka keɓe don jigilar mai a halin yanzu ya tsaya cak.
An sanar da jakadan kasar China da ke kasar Benin, Peng Jingtao, tare da hukumar kula da bututun mai, Wapco, a hukumance kan wannan takunkumin.
Read Also:
Ana gudanar da hada-hadar da ta kai na kuɗi sama da CFA biliyan 600 ta hanyar bututun man na Nijar wanda ya ratsa ta cikin ƙasar Benin.
Gamayyar kamfanonin kasar Sin ne suka samar da bututun man mai tsawon kilomita 2,000 da kuma rijiyoyin mai na kasar Nijar.
An kammala aikin bututun man fetur ɗin wanda ake sa ran zai rika jigilar ganga 90,000 na mai a kowace rana zuwa tashar fitar da kaya a kasar Benin a farkon wannan shekarar.
Sai dai kuma rashin jituwar da ke tsakanin ƙasashen biyu bayan juyin mulkin watan Yulin 2023 da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum na iya kawo cikas ga aikin.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 17 minutes 4 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 58 minutes 29 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com