An samu rahoton mutum 44 sun kamu da cutar kwalara a lardin Tana River da ke Kenya yayin da ambaliyar ruwa ke ƙara buɗe ƙofar yaɗuwar cututtukan da ake iya ɗauka ta ruwa.
Sanarwa da Hukumar lafiya ta duniya ta fitar wadda ta bayyana adadin, inda ta ce hukumomi a Kenya tare da goyon bayan WHO da kuma sauran hukumomi na sa ido a kan cutar da matakan da za a ɗauka a faɗin ƙasar yayin da ake fama da ambaliyar.
Ambaliyar ta shafi kashi ɗaya cikin huɗu na mutane miliyan ɗaya tare da samun rahoton mutuwar mutum 238 a faɗin ƙasar. Tana River na ɗaya daga cikin lardunan da ambaliyar ta fi shafa a Kenya.
A ranar Talata ne babbar sakatariyar lafiya ta Kenya Mary Muthoni ta ce akwai babbar barazana na yiwuwar cututtukan da ke yaɗuwa ta ruwa su zama annoba idan ba a ɗauki mataki da wuri ba.
Read Also:
Ms Muthoni ta yi magana ne yayin da ita da sauran jami’an lafiya suke raba kayayyakin tsabtace ruwa a babban birnin Nairobi.
Ta kuma yi magana a kan haɗarin cututtukan da ake samu a lalataccen abinci da abincin da aka samu daga hanyoyi marasa nagarta da ambaliyar ta janyo ƙaruwarsu.
WHO ta ce za ta ci gaba da ba da goyon baya ga matakan gaggawa na gwamnati kuma za ta “ci gaba da sa ido kan ɓarkewar cututtuka da ka iya saurin yaɗuwa idan ba a yi saurin magance su ba”.
Ta kuma ce, “WHO ta kuma samar da kayayyakin magance cutar ta kwalara da ake rarrabawa a muhimman larduna wanda za su iya warkar da mutum 10,000”.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 23 minutes 31 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 18 hours 4 minutes 56 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com