Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya miƙa ta’aziyarsa a kan rasuwar Hakimin Gatawa Alhaji Isa Muhammed Bawa, wanda ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane.
A saƙon jajen, gwamnan ya ce yana miƙa saƙon jajensa zuwa ga iyalan marigayin da mutanen Sabon Birni da dukkan mutanen jihar.
Cikin wata sanarwa da Sakataren Watsa Labaransa, Abubakar Bawa ya fitar, Aliyu ya ce gwamnatinsa ba za ta huta ba har sai an kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a jihar.
Gwamna Aliyu ya bayyana kisan a matsayin “rashin tausayi da dabbanci”, wanda dole a yi Allah-wadai da shi.
Sanarwar ta bayyana mamacin a matsayin mai gaskiya da amana, da son zaman lafiya wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen aiki ga al’umma.
Dokta Aliyu ya yi kira ga jami’an tsaro a jihar da su ƙara ƙoƙari a kan wanda suke yi domin tabbatar da tsaro a jihar, sannan su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa an kama waɗanda suka kashe hakimin domin su fuskanci hukunci.
Tuni dai Al’ummar garin Sabon Birni a jihar suka gudanar da sallar janazar Sarkin Gobir na Gatawa, Isa Bawa da safiyar yau Alhamis, bayan kashe shi da ƴan bindiga suka yi.
Labarin kisan sarkin ya ɓulla ne a ranar Laraba, bayan da bayanai suka tabbatar da cewa ƴan bindigar sun halaka shi duk da neman kuɗin fansa da suka yi.
Ɗaruruwan mutane ne suka hallara domin gudanar da sallar a garin Sabon Birni.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 44 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 42 minutes 9 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com