Home General Mutane 3 sun mutu a rikicin ‘yan Shi’a da ‘yan sanda a...

Mutane 3 sun mutu a rikicin ‘yan Shi’a da ‘yan sanda a Abuja

An kashe ‘yansanda biyu da jikkata wasu biyu, sannan kuma wani ɗan kasuwa ya rasu bayan da aka harbe shi a wani rikici da ya tashi tsakanin da ‘yan Shi’a na ƙungiyar Harka Islamiyya a Najeriya, (IMN), mabiya Sheik Ibrahim El-Zakzaky, a kasuwar Wuse da ke Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutumin da aka harbe mai suna Amiru, an harbe shi a ƙirji ne lokacin da ‘yansanda suke rarakar masu zanga-zangar na Shi’a.

Jaridar ta ce wani da y ga abin da ya faru wanda ya nemi da kada a fadi sunansa ya ce an garzaya da mutumin asibitin Wuce Zone 3 inda a can ya ga ‘yansanda da dama da aka jikkata a rikicin, a don haka aka nufi asibitin Maitama da shi inda a kan hanya ya cika.

Mabiya kungiyar ta IMN dai na zanga-zangar da suke yi wa lakabi da Arbaeen, wato cika kwana arba’in bayan taron Ashura.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan babban birnin SP Josephine Adeh, ta fitar, ta tabbatar da kisan jami’ansu guda biyu da jikkata wasu biyu tare kuma da kona motocin ‘yansanda na sintiri uku a rikicin wanda ta ce ba gaira ba dalili mabiya kungiyar suka kai wa jami’ansu hari.

A sanarwar da ‘yansandan suka fitar sun ce, ”mabiya haramtacciyar kungiyar sun kai wa wajen binciken ababan hawa na ‘yansanda hari haka kawai, dauke da adda da bama-bamai hadin gida wadanda aka yi da kananzir a cikin kwalba, da kuma wukake.

Rundunar ta ce an kama mutane da dama, inda kwamishinan ‘yansandan birnin na Abuja CP Benneth C. Igweh, ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
COAS Ya Bukaci Bojojin Nijeriya da su Mayar da Hankali Wajen Kare Rayukan Fararen HulaTURA TA KAI BANGO: Bayan Mutuwar Bashar Sani, Dole ne Arewa Ta Fuskanci MatsalolintaDangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara
X whatsapp