Ma’aikatar lafiyar Lebanon ta ce wasu jerin gwanon hare-haren da Isra’ila ta kai mata sun yi sanadiyar mutuwar mutum 22, sannan mutum 117 suka jikkata.
An kai hare-haren ne a Bachoura, wanda su ne hare-hare mafiya muni tun farkon fara yaƙin.
Wasu kafofin sadarwa a ƙasar sun ce Wafiq Safa – wanda na hannun damar jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah ne, wanda kuma ake tunanin shi ne Isra’ilar take hari – ya tsira daga harin.
Har yanzu da rundunar sojin Isra’ila da Hezbollah babu wanda ya ce komai a game da hare-haren.