An samu ƙaruwar gobara a Kano saboda shigowar sanyi

Hukumar kashe gobara a Kano ta ce an samu ƙarin tashin gobara a faɗin jihar sakamakon shigowar yanayin hunturu a wasu yankunan a jihar.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Kakakin hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar aka raba manema labarai a a jihar da ke arewa maso yammacin Nijeriya in da ya ce kafin zuwan yanayin hunturun an samu raguwar tashin gobara a jihar – wadda ita ce cibiyar kasuwancin arewacin ƙasar.

Saminu Yusuf Abdullahi ya ce a watan Nuwamban da ya gabata kaɗai an samu tashin gobara a jihar har sau 43, sakamakon yadda mutane ke ƙara ta’ammali da wuta a lokacin na hunturu.

”Adadin ya ninka, domin a watan Oktaba an samu matsalar tashin gobara a Kano sau 24, amma sakamakon shigowar hunturu a watan Nuwamban adadin ya kai 43”, in ji shi

Ya kuma ce daga shigowar watan Disamba, zuwa yanzu hukumarsu ta samu labarin tashin gobara har sau bakwai, zuwa yanzu.

Haka kuma hukumar kashe gobarar jihar ta ce mutum uku sun mutu, yayin da aka yi asarar dukiya da ta kai naira miliyan 130, a cikin watan da ya gabatan sakamakon tashin gobarar.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1487 days 2 hours 19 minutes 36 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1469 days 4 hours 1 minute 1 second

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com