PDP ta yi watsi da kasafin kudin 2025

Jam’iyyar PDP ta soki kasafin kuɗin da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar, wanda ta bayyana a matsayin wani abu da ”ba zai yiwu ba” kuma wanda ”babu gaskiya a ciki”.

Sakataren yaɗa labaran PDP Debo Ologunagba, a cikin wata sanarwa a kan kasafin kuɗin, ya ce kasafin kuɗin ya shafi abubuwan da za su ƙara jefa jama’a cikin ƙangin talauci da kuma matsalar tsaro.

Shugaba Tinubu ya gabatarda kasafin na 2025, na naira tiriliyan 49.7 ga majalisar dokokin Najeriya, inda ya sha alwashin bayar da fifiko ga ɓangaren da samar da ayyukan raya ƙasa da fannin kiwon lafiya da kuma ilimi.

Sai dai jam’iyyar PDP mai adawa a ƙasar ta ce gabatar da kasafin kuɗin ba wani abu bane illa alƙawurran da ba za a iya cikawa ba.

Jma’iyyar adawan da zargi gwamnatin shugaba Tinubu da gazawa wajen samar da muhimman abubuwan more rayuwa ga jama’ar ƙasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com