Home General Gwamnatin Jihar Kano ta magantu Kan dokar harajin Tinubu

Gwamnatin Jihar Kano ta magantu Kan dokar harajin Tinubu

Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana matsayarta kan sabbin dokokin haraji da ake tattaunawa a Majalisar Dokokin Najeriya.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan ne lokacin bikin sabuwar shekarar 2025 da aka gudanar a Filin Mahaha da ke Ƙofar Naisa.

Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na mataimakin gwamnan Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar, Gwarzo, ya ce “Waɗannan dokokin haraji ba su ne mafita ga matsalolin tattalin arziƙinmu ba”.

Ya ƙara da cewa jihar Kano ba zata yarda da kowace doka da za ta cutar da walwalar al’ummarta ba.

Ya yaba wa jajircewar al’ummar Kano wajen fuskantar ƙalubalen tattalin arziƙi, inda ya ce sam harajin bai dace ba.

Ya ƙara da cewa kamata ya yi gwamnati ta fi mayar da hankali kan yaƙi da talauci da yunwa, musamman a yankin Arewa, wanda ke fama da tsadar rayuwa da rashin tsaro.

Mataimakin Gwamnan, ya na jaddada nasarorin gwamnatin Kano a ɓangarorin lafiya, ilimi, samar da hanyoyi, da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp