Tinubu ya buƙaci hukumar FRSC ta kare haɗurran tankokin mai

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumar kare hadurra ta kasar FRSC, da hukumomin da ke kula da dokokin kan hanya su dauki matakan kariya kan hadurra da fashewar tankokin mai a kasar, kamar yadda.

Ana yawan samun hadurran fashewar tankar mai a sassa daban-daban na Najeriya lamarin da ke haddasa mutuwar gwamman mutane da jikkatar wasu da dama baya ga salwantar dukiya.

Ko a ranar Lahadin karshen mako, wata tankar mai ta fashe a yankin Ugwu Onyeama da ke titin birnin Onitsha na Enugu, inda hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum 18 da jikkatar wasu da dama.

Ana danganta yawan hatsarin motoci a Najeriya kan tukin ganganci da gudu fiye da kima da direbobi ke yi, da rashin kyawun tituna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com